TAURARIN FINA-FINAN HAUSA……
Shiri Na Uku….
Mai karatu barka da warhaka, da fatan kana cikin koshin lafiya.
Acikin shirin namu na yau, mun sami tambayoyi daga wasu mutane kamar haka:-
@Aliyu Ahmad.
@Basira Dalladi.
@Hafsat Bauchi.
@Zailani Zaria.
@Murtala Sokoto.
@Zainab Mauduguri.
Wadanda suke son Jin tarihin Shahararriyar Jarumar Fina-Finan Hausa ta Kannywood, HADIZA ALIYU GABON.
Jaridar Mikiya ta sami damar tattaunawa da ita, ga dai yadda tattaunawarsu ta kasance da wakilin Mikiya…..
Mikiya: Wacece Hadiza Aliyu Gabon?
Gabon:: To Bismillahir rahmanirrahim, Ni dai sunana Hadiza Aliyu Gabon, An haifeni a ranar 1 ga watan Yuni na shekarar 1989 a kasar acikin garin Libreville a jamhuriyar Gabon.
A bangaren Mahaifiyata Kuma Ni Ina daga cikin zuriyar Fulani ce daga Jahar Adamawan Nigeria.
Na yi makarantar Primary da Secondary a kasata ta haihuwa. Sannan na rubuta jarrabawata ta sakandare tare da burin zama babbar Lauya, Sai dai bayan na fara karatun, tilas tasa na fice daga makarantar, saboda wasu batutuwan da suka kawo cikas ga karatun nawa. Amma Kuma daga baya na samu
damar halartar wata makarantar ta daban, inda na samu na sami takardar Difloma a Harshen Faransanci. Daga nan kuma sai na fara koyar da harshen faransanci a wata makarantar kudi.
Mikiya::: Yaushe kika fara harkar fim?
Gabon:: Bayan na bar kasar Gabon, sai na dawo garin Kaduna da zama a wajen yayata, inda Kuma na nuna mata sha’awata ta shiga harkar Hausa Fim, tabbas ta bani kwarin gwiwwa sosai, A haka dai na Fara har Kuma Allah ya hadani da sarki
Ali Nuhu, inda Kuma na nemi taimakonsa don cikar burina na zama Jaruma, cikin hukuncin Allah Ali Nuhun ya shiryamin fim mai suna ARTABU a shekarar 2009.
Mikiya:: Shin me yaja hankalinki zuwa ga harkar fim?
Gabon::Eh to Ni dai har ga Allah na fahimci harkar fim, harkace ta fadakarwa da Nishadantarwa, kuma harka ce wacce mutum zai iya dogaro da kansa.
Mikiya:: Daga wane lokaci ne tauraruwarki ta fara haskawa?
Gabon::Tauraruwata ta fara haskawane, tun daga lokacin da fuskata ta bayyana a fim din #Artabu da #’YarMaye da sauransu.
Mikiya:: A tunanin ki wane irin kallo masu kallonku suke muku?
Gabon:: Tabbas Ni na san da cewar akwai masu yi mana mummunan zato, Amma kuma na san da akwai masu yi mana kyakkyawan zato, dama haka duniyar take.
Mikiya:: Amma a tunaninki me yasa ake yi muku mummunan zato?
Gabon:: Saboda akwai wasu daga cikinmu, wadanda suke ja mana zagi, Amma abunda nake so mutane su sani shine, a duk inda al’umma ta hadu zaka samu akwai Nagari, Sannan Kuma akwai Na banza. Saboda haka don Allah a rinka kyautatawa juna zato.
Mikiya:: Waye Uban gidanki a kannywood?
Gabon:: Daddy na, wato Ali Nuhu.
Mikiya::Waye saurayinki a kannywood?
Gabon:: hhhhhhhhhhh bani da saurayi.
Mikiya::: Ance Kina Soyayya da Naziru Sarkin Waka?
Gabon:: A’a wannan maganar ba Gaskiya bace, akwai dai mutunci tsakanina da Naziru Amma babu Soyayya a tsakanin mu.
Mikiya::: A cikin Fina-Finan ki wannene yafi burge ki?
Gabon::Dukkan Fina-Finan dana fito acikinsu, wallahi suna burgeni.
Mikiya::Ina kike samun kudaden da kike tallafawa marayu da marasa galihu?
Gabon:: Ina samun kudaden ne ta hanyar Gidauniyata.
Mikiya:: Meye babban burinki a rayuwa?
Gabon: Babban burina a rayuwa shine, inga Nayi aure, na mallaki zuri’a tawa ta kaina, Sannan Yana daga cikin burina in ga na sami dukiya mai yawa wacce zan iya cigaba da taimakawa marayu da marasa galihu.
Mikiya:: Shin kin taba samun lambar girmamawa?
Gabon:: Eh na samu lambobin yabo marasa iyaka.
Mikiya::Shin kina aikin jakadanci?
Gabon:: Eh Ina aikin jakadanci a Kamfanin M.T.N da kuma Kamfanin Indomie.
Mikiya:: Yaushe ne zaki yi aure?
Gabon: Duk lokacin da Allah ya kawo Miji Nagari, Mai tsoron Allah da rikon amana.
Mikiya:: Wacce shawara zaki bawa masoyanki?
Gabon:: Shawarata itace dasu dage da yimin addu’a, Sannan Kuma dasu cigaba dayi mana uzuri, Musamman inda mun hadu da juna.
Mikiya:: Wacce shawara zaki bawa masu son shiga harkar fim?
Gabon::Shawarata itace, su zamo masu hakuri da juriya, Sannan su zamo masu biyayya ga manyansu, Sannan Kuma su zamo masu kiyaye mutumcin kansu dana gidan da suka fito.
Mikiya:: Hajiya Hadiza Aliyu Gabon Muna Godiya da lokacin da kika bamu.
Gabon:: Nima na gode, Ina addu’ar Allah ya kara daukaka Jaridar Mikiya da ma’aaikatanta.
Wannan itace karshen tattaunawarmu da Jaruma Hadiza Aliyu Gabon.
Kuma zaku iya aiko da sakonnin tambayoyin ku ta Lambarmu ta Whatsapp kamar haka::08138968615.
A Madadin Shugaban shirin M.Inuwa MH, Sai Wanda Ya Tsara Shirin Sabi’u Danmudi Alkanawi, Sai Ni Dana Gabatar muku da shirin SUNUSI (D) DANMALIKI Nake cewa sai mun hadu a wani satin.