Shirye-shirye

Taurarin Fina-finan Hausa: Nafi Son Ahadani Fim Da Fati Washa, Inji Nuhu Abdullahi.

Spread the love

Mai karatu barka da war haka, barka da sake saduwa damu acikin sabon shirin mu Taurarin Fina-finan Hausa.

A yau zamu kawo muku tattaunawar mu da Tauraro, Jarumi, Kuma Mai Shiryawa Wato NUHU ABDULLAHI.

Ga dai yadda hirar tamu dashi ta kasance….

Mikiya: Shin wanene Nuhu Abdullahi?

Nuhu: To Ni dai sunana Nuhu Abdullahi, An haifeni a shekarar 1981 a cikin birnin Kano, anan nayi karatuna na Primary da Secondary da kuma makarantar gaba da Secondary.

Mikiya:Shin me yaja hankalin ka zuwa ga harkar fina-finan Hausa?

Nuhu:To Ni dai tun ina yaro mutum ne Mai son neman na kansa, hakan yasa lokacin girma, sai nayi tunanin irin sana’ar da zanyi domin dogaro dakai, kawai sai naga sana’ar fim ai sana’ace wacce in mutum ya zuba jari, zai iya samun riba, hakan yasa sai na shiga harkar, Kuma Ni na shigeta ne da jarina, inda na fara shirya fim na kaina, to da haka dai aka fara.

Mikiya: A matsayinka na Mai shirya fim, ya akayi kuma ka fara fitowa a matsayin dan wasa?

Nuhu: Eh to, wato har ga Allah Ni banzo da niyyar fitowa a fim ba, Amma daga baya sai Aminu Saira Wanda shi Director ne, shine mutumin da yayi karfafamin gwiwwa akan cewa na fara fitowa, to daga nan sai na amshi shawararsa.

Mikiya:Da wanne fim ka fara fitowa?

Nuhu:Da fim din ASHABUL KAHFI, Fim ne na Malam Aminu Saira.

Mikiya:Waye Mai gidanka a kannywood ?

Nuhu:Malam Aminu Saira, Shine uban gidana a harkar fim.

Mikiya:Da wacece kafi son a hadaka aikin fim da ita?

Nuhu: Himmmm Gaskiya nafi son aikin fim da Fati Washa.

Mikiya:Me yasa kafi son aiki da Fati Washa?

Nuhu:Saboda akwai kyakkyawar fahimtar juna a tsakanina da ita.

Mikiya:Shin Nuhu Abdullahi yana da iyali?

Nuhu:Hmmm A’a har yanzun banyi aure ba.

Mikiya:A cikin fina-finan ka wanne ka fiso?

Nuhu: Gaskiya nafi son fim din Kanin Miji.

Mikiya:A wacce shekara ka fara fitowa a fim?

Nuhu:Na fara fitowa fim a shekarar 2013.

Mikiya:Shin banda harkar fim kana wata sana’ar?

Nuhu:Eh Ina harkar Noman Masara da Shinkafa, da sauran kayan Noma.

Mikiya:Shin Nuhu Abdullahi Dan wacce Jam’iyya ce?

Nuhu:To Ni dai ina cikin jam’iyyar A.P.C ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Mikiya:Me yasa kake bin tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari?

Nuhu:Saboda na Yarda da gaskiyar sa da rikon amanar sa. Kuma Ina da yaki nin cewa Muhammadu Buhari zai kai Nigeria ga tudu min tsira.

Mikiya:Wacce shawara zaka bawa Shugaba Buhari akan harkar tsaron Nigeria?

Nuhu:Shawarata itace “A kyautata yanayin jami’an tsaron mu, Sannan a samu hadin kan sarakunan gargajiya.

Mikiya:Waye Babban abokinka a kannywood?

Nuhu:Babban abokina shine Marubucin Fina-finan Hausan nan, wato IBRAHIM BIRNIWA

Mikiya:Wane abune yake yawan bata maka rai a duniya?

Nuhu:Idan naga matashi yana harkar shaye-shaye.

Mikiya:A duk lokacin da kaji ana zagin ‘yan fim ya kake ji?

Nuhu: A zahirin gaskiya bana jin dadi, kuma abun yana min ciwo sosai, duk da dai nasan wasu ke jama wasu zagin, Amma don Allah ina bawa mutane shawarar a daina yi Mana kudin goro, duk al’ummar daka gani, ya zama dole a samu na kirki dana banza.

Mikiya:Yaushe masu kallon ka zasu sake ganin sabon fim dinka?

Nuhu:Insha Allahu Kwanan zasu ga sabon fim dina mai suna LABARINA

Mikiya: Yaushe Nuhu zai yi aure?

Nuhu:Insha Allahu kwanannan.

Mikiya:Me zaka cewa masoyan ka?

Nuhu:Ina godiya da irin kaunar da suke min.

Mikiya: To Malam Nuhu Abdullahi anan tattaunawar mu dakai tazo karshe, Saboda haka muna godiya da Lokacin daka bamu.

Nuhu:Ni keda godiya, Nagode sosai, Allah ya kara daukaka Jaridar Mikiya.

Kuma zaku iya aiko da sakon tambayar ku ta WhatsApp Number mu kamar haka: 08138968615.

A madadin shugaban shirirn M.Inuwa M.h, Sai Wanda ya tsara shirin Sabi’u Yakubu Alkanawyy, Sai Ni dana kawo muku shirin Sunusi (D) Danmaliki nake cewa sai mun hadu a wani satin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button