Shirye-shirye

TAURARIN FINA-FINAN HAUSA……

Spread the love

Shiri Na Farko….

Mai karatu barka da warhaka, da fatan kana cikin koshin lafiya. Acikin shirin namu na yau mun sami tambayoyi daga wasu mutane kamar haka:-
@Habiba Dayyabu Yola.
@Zainab Yola.
@Bashir Keffi.
@Madugu Sani.
@Lawal Aliyu.
Wadanda suke son Jin tarihin Shahararriyar Jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Hafsat Idris (Barauniya). Jaridar #Mikiya ta sami damar tattauna da ita, ga yadda tattaunawarsu ta kasance da wakilin Mikiya…..

Mikiya: Wacece Hafsat Idris?

Hafsat: To nidai sunana Hafsat Idris, kuma an haifeni a garin Kano, amma kuma na girma a garin shagamu, daga baya kuma muka dawo Kano da zama.

Mikiya: Ko zaki iya fada mana shekarunki?

Hafsat: Hmmmm a’a, wannan wani sirri ne nawa, wanda na barwa zuciyata.

Mikiya: Shin me yaja hankalinki zuwa ga harkar Fim?

Hafsat: Saboda na fahimci harkar Fim hanya ce ta isar da sako ga al’umma, sannan kuma harkar fim sana’a ce wacce take kawo kudi sosai, domin bana zaton cewa ko ma’aikacin gwamnati zai samu abunda nake samu a wata. Hakan yasa na shigeta gadan-gadan, kuma na riketa hannu biyu-biyu.

Mikiya: Daga wane lokaci ne tauraruwarki ta fara haskawa?

Hafsat: Taurarona ya fara haskawa ne tun daga lokacin dana bayyana a fim din #Barauniya. Fim din Barauniya shine fim na musanman da ya haskaka ni, kuma ya zama silar daukaka ta a harkar fim.

Mikiya: Ya kike ji idan aka ce ‘yan fim ‘yan iska ne?

Hafsat: Hmmm Gaskiya nakan ji babu dadi, kuma raina yana matukar baci, a duk lokacin dana ji ana mana kudin goro, tabbas masana’antar kannywood masana’anta ce wacce ta kunshi dubban al’umma, akwai Nagari akwai kuma Na banza, saboda haka don Allah adaina yi mana kudin goro gaba daya.

Mikiya: Ya maganar aure?

Hafsat: Eh na taba yin aure, kuma har na haife yara, amma Yanzun kam bani da aure, Amma insha Allahu zanyi aure kwananan.

Mikiya: Yaranki Nawa?

Hafsat: Hmmm wannan wani sirrine nawa.

Mikiya: Wanda zaki aura shima Dan Fim ne?

Hafsat: A’a, ba ya harkar Fim.

Mikiya: Shin kin tabasamun kambun girmamawa?

Hafsat: Eh an zabenii a matsayin jarumar Kannywood da tafi fice a shekarar 2017 daga kamfanin dilancin
shiri na City People Movie Awards.

Mikiya: Shin kema kina shirya fim na kashin kanki?

Hafsat: Eh Ina shirya nawa na kashin kaina, a karkashin kamfanina mai suna Ramlat Investment.

Mikiya: Wane fim ne kika taba shiryawa naki na kashin kanki?

Hafsat: Nice na shirya fim din #Kawaye, Wanda na saka manyan Jarumai irinsu Ali Nuhu, Sani Danja, Hajara Usman da sauransu.

Mikiya: Wadane fina-finanki ne suka fi burge ki?

Hafsat: Eh suna da yawa, amma acikin su akwai fim din #BikiBuduri da #Furuci da #Labarina da #Barauniya da #Makaryaci da #Abdallah da #Rumana da #ZanRayuDaKe da #NamijinKishi da #RigarAro da ‘#YarFim da #kawayenAmarya da #BarristaSurayya da sauran su.

Mikiya: Wacce shawara zaki bawa masu son shigowa harkar fim, musamman mata?

Hafsat: Shawarata itace su zamo masu hakuri da juriya, sannan su zamo masu biyayya ga manyansu, sannan kuma su zamo masu kiyaye mutumcin kansu dana gidan da suka fito.

Mikiya: Hajiya Hafsat muna godiya da lokacin da kika bamu.

Hafsat: Nima na gode, Ina addu’ar Allah ya kara daukaka Jaridar Mikiya da ma’aaikatanta.

Wannan itace karshen tattaunawar mu da jaruma Hafsat Idris.
Kuma zaku iya aiko da sakonnin tambayoyin ku ta Lambarmu ta Whatsapp kamar haka: 08138968615.

A Madadin Shugaban Shirin M.Inuwa MH, Sai Wanda Ya Tsara Shirin Sabi’u Danmudi Alkanawi, Ni Dana Gabatar Sunusi Danmaliki Nake Cewa Sai Mun Hadu A Wani Satin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button