Tawagar Buhari sun Isa jihar Borno domin ta’aziyya.
Tawagar Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ta isa Maiduguri, Jihar Borno a ranar Litinin a ziyarar jaje game da kisan da ’yan ta’adda suka yi wa manoma a karshen mako.
Ku tuna cewa a karshen mako, Mayakan Boko Haram sun fille kan manoman shinkafa akalla 43 a Zabarmari, jihar Borno, kimanin kilomita 20 daga Maiduguri, babban birnin jihar.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana harin a matsayin “hari mafi karfi” da aka yiwa fararen hula a shekarar 2020. An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba Shugaban Majalisar Dattawa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi ya sanya wa hannu ranar Litinin.
A cewar sanarwar, mambobin tawagar sun hada da Shugaban Ma’aikata na Shugaban kasa, Ibrahim Gambari; Ministocin Babban Birnin Tarayya, Mohammed Bello; Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Ali-Pantami, da Karamin Ministan Noma, Mustapha Baba-Shehuri.
Sauran sun hada da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, da kuma babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban kasa, Garba Shehu. Mataimakin gwamnan jihar Borno, Usman Umar Gadafu ne ya tarbi tawagar a lokacin da suka isa filin jirgin.
Tawagar tana Borno, a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya, domin jajantawa da kuma sanin dangin wadanda abin ya shafa, da Gwamnati, da kuma mutanen jihar ta Borno kan lamarin.