Tawagar Majalisar Dattawa Sun Ziyarci Borno Sun Gana da Gwamnan.

Spread the love

Daga Ahmed T. Adam Bagas

A Yau Litinin ne Tawagar Wakilan Majalisar Dattwan Nigeria suka Ziyarci Maiduguri domin Ganawa da Gwamnan Jahar Farfesa Babagana Umara Zulum.

Tawagar karkashi Jagorancin Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Sanata Yahaya Abdullahi, Shugaban Ma’aikatan Majalisar Sanata Orji Uzor Kalu.

Sauran Sun Hada da Sanata Yahaya Alhaji. Yawu, Sanata Kashim Shattima, Sanata Muhammad Ali Ndume da Sanata Abubakar Kyari.

Sanatocin Sun Gana da Gwamna Zulum a Gidan Gwamnatin Jahar Borno kan Matsalar Kashe-Kashen da Yan Boko Haram sukayi `yan Kwanakin nan a Jahar.

Shugaban Masu Rinjayen a Madadin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan ya Bada Tabbacin Za’a Magance Matsalar Boko Haram Nan bada Dadewa ba, Lawan din yace Ya samu Ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kan Matsalar Boko Haram domin Haka za’a Dauki kwararan Matakai domin kawo karshen Ta’addaccin Boko Haram a Jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *