Kasashen Ketare

Tawagar Masu Shiga Tsakani Ta Kasashen Yammacin Afrika Ta Isa Kasar Mali.

Spread the love

Tawagar wacce tsohon shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan yake jagoranta ta isa kasar Mali a jiya Asabar, domin haduwa da masu juyin mulkin kasar da suka kifar da gwamnatin Ibrahim Bubakar Keita.

Tawagar ta sami tarba daga mataimakin sabon shugaban mulkin kasar aksar, Malick Diaw da kuma kakakin gwamnatin sojan, Isma’ila Wague.

Juyin mulkin na kasar Mali ya haifar da fargaba da zullumi a cikin kasashen makwabta kamar Niger da Burkina Faso, da suke fama da matsalar masu dauke da makamai.

A makon da ya wuce ne dai sojojin kasar Malin suka tilasta wa shugaban kasar Ibrahim Bubakar Keita yin murabus daga mukaminsa na shugabancin kasar.

Daga Haidar H Hasheem Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button