Labarai

Tinubu bai damu da hukuncin kotun ba, ya yi imani da adalcin shari’a – Fadar Shugaban Kasa

Spread the love

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa Bola Tinubu, ya ce shugaban nasa bai damu da yiwuwar sakamakon hukuncin kotun zaben shugaban kasa ba.

Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, Ngelale ya ce Tinubu na ganin bai kamata ya tsaorata da jami’an shari’a ba game da batun zaben.

Tun da farko a ranar litinin, kotun ta saka ranar 6 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan kararrakin da ke kalubalantar nasarar Tinubu a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Jam’iyyun Allied Peoples Movement (APM), Peter Obi na Labour Party (LP), da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP sun tunkari kotun domin kalubalantar nasarar Tinubu.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce Tinubu na da kwarin gwiwar cewa kwamitin zai yanke hukunci bisa ga hujjojin da aka gabatar.

Ya ce shugaban kasa yana da “kwarin gwiwa da imani” a bangaren shari’a, inda ya kara da cewa Tinubu na da tabbacin cewa za a tabbatar da aikinsa.

“Ba kamar wasu ‘yan siyasa a kasarnan ba, shugaban kasa yana ganin babu bukatar yin barazana ga jami’an shari’a,” in ji shi.

“Yana ganin babu bukatar yada jita-jita game da amincin jami’an shari’a. Ya yi imani da tsarki da amincin tsarin shari’ar Najeriya.

“Ya yi imanin manyan maza da mata da ke cikin kwamitin za su yanke shawararsu ne kawai a kan abubuwan da ke gabansu ba bisa wani abu ba.

“Sakamakon kwarin gwiwa da imaninsa ga bangaren shari’a, ya yi imanin cewa wa’adin da ‘yan Najeriya suka ba shi a lokacin zabe zai tsaya. Matsayin shugaban kasa kenan.

“Zai ci gaba da tabbatar da cewa ko da menene sakamakon hukuncin zai yi, a nasa bangaren kuma ya tabbatar da cewa hukumominmu sun ci gaba da mutuntawa, ba wai ga shi kadai ba, har ma da dukkan ‘yan takarar.

“Bai damu ba saboda ya san ya ci zabe. Mun yi imanin cewa mun gabatar da mafi kyawun shari’ar kuma shaida tana kan mu. “

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button