Labarai
Tinubu ya cancanci yabo saboda dakatar Ministar Jin Kai Betta Edu – Atiku
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yabawa shugaba Bola Tinubu kan dakatar da ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu ta yi.
A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Talata, Atiku ya lura cewa dakatar da ministar abin yabawa ne amma bai wadatar ba.
Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ne Shugaba Bola Tinubu, ya umurci Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Ola Olukoyede, da ya binciki duk wata hada-hadar kudi da ta shafi ma’aikatar Agaji da Rage Talauci ta Tarayya.