Labarai

Tinubu ya gana da Ganduje da Hafsoshin Tsaro kan rikicin manoma da makiyaya

Spread the love

A yau Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa da hafsoshin tsaro a fadar Aso Rock Villa.

Taron wanda aka gudanar a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, ya shafi nemo bakin zaren warware rikicin da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a sassan kasar nan.

“Shugaba Bola Tinubu na shirin karbar rahoto da tsari daga mambobin kwamitin kasa kan gyare-gyaren dabbobi da magance rikice-rikice masu nasaba da juna a Najeriya,” in ji Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) a shafin X.

Kafin ya kammala wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Kano, Ganduje ya yi aiki da masu ruwa da tsaki wajen ganin an magance matsalar.

A watan Janairu, Ganduje ya kaddamar da wani kwamiti da aka dorawa alhakin shirya taron kasa wanda zai samar da mafita ga rikicin manoma da makiyaya.

Kwamitin mai mambobi 26 ya kasance karkashin jagorancin Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Da yake jawabi a wurin taron, Ganduje ya ce kwamitin Jega ya mika rahotonsa wanda ya ce maganin rikicin ne.

“Shugaban kasa, na gamsu cewa rahoton da aka kawo muku a yau yana da maganin matsalolin da ke addabar kiwo,” in ji tsohon gwamnan.

“Yana magance mahimman sauye-sauye tare da gabatar da zaɓuɓɓukan ci gaba daban-daban da ake buƙata don ci gaba mai dorewa a fannin.

“Shawarwarin za su inganta samar da kayayyaki, inganta rayuwa, inganta kiyaye muhalli, magance matsalolin da ke haifar da rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma taimakawa wajen rage tsadar shigo da kayayyakin dabbobi kamar madara da naman sa.”

A cikin shekarun da suka gabata an yi asarar rayuka da amfanin gona da dabbobi sakamakon rikicin makiyaya da manoma a sassa da dama na kasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button