Labarai

Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa don samun sabon bashin dala biliyan 8.6, da €100m.

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawa ta amince da ya karbo sabon rancen dala biliyan 8.6 da kuma Yuro miliyan 100 da aka ware domin gudanar da muhimman ayyuka a sassa daban-daban na tattalin arziki.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wata takardar bukatar da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta a farkon zaman majalisar a ranar Talata.

Shugaban ya yi karin haske a cikin wasikar cewa bukatar sa na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na karbar rancen kasashen waje na 2022-2024 da gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da shi.

Ya kara da cewa ayyukan da za a gudanar da bashin an kayyade su ne bisa la’akari da tattalin arziki da kuma gudummawar da ake sa ran wajen ci gaban kasar.

“Majalisar Dattawa za ta so ta lura cewa gwamnatin da ta shude ta amince da shirin karbar bashi na 2022-2024 da Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta gudanar a ranar 15 ga Mayu, 2023.

“Aikin ya rataya ne a dukkan bangarori, tare da mai da hankali musamman kan ababen more rayuwa, noma, kiwon lafiya, samar da ruwan sha, hanyoyi, tsaro da samar da ayyukan yi da kuma sake fasalin harkokin kudi.

“Saboda haka amincewar da ake buƙata tana cikin jimlar $8,699,168,559 da Yuro miliyan 100.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button