Labarai

Tinubu Ya Yabawa Hajiyar Nan Data Tsinci N60,000,000 ta Dawowa Masu Kuɗi Abinsu.

Spread the love

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna matuƙar jin daɗi da godiya ga baiwar Allah Hajiya Aisha Yan Guru abisa abin ayaba data nuna a ƙasa mai tsarki.

Matar mai tsananin tsoron Allah daga Karamar Hukumar Bunguɗu dake jihar Zamfara dai ta dawo da dala $80,000 ne ga masu su ne, a yayin gudanar da hajjin bana.

Masana canjin kuɗi dai sunyi ittifaƙin cewar, kuɗin zai kai kimanin N60,000,000 na kuɗin Najeriya.

Wannan yabon dai ya fito ne daga bakin shugaban hukumar alhazzai ta jihar Zamfara, Alhaji Musa Mallaha, a ofishin sa dage Gusau yayin fayyace abubuwan nasara da aka cimma a lokacin gudanar da aikin Hajji na 2023.

Alhaji Musa Mallaha ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin Zamfara daga nata ɓangaren na ƙoƙarin haɗa yar ƙwarya ƙwaryan liyafa domin karrama wannan mata mai tsoron Allah. Rahoton The Punch.

Mallaha yace, sanda labarin ya ƙarade kafafen sadarwa, shugaban ƙasa ya cika da murna, inda nan take ya bada umarnin ayi hira da ita a gidan talabijin na ƙasa domin a ajiye tarihin bajintar tata, amma an riga da an dawo da ita Najeriya a lokacin. Rahoton Daily Trust.

Jaridar Vanguard ta ruwaito ofishin matar gwamnan jihar ta Zamfara zai shirya taro domin karrama matar a bisa halin ƙwarai data nuna a matakin jiha, wanda ake fatan gwamnan jihar zai halarta.

A cewar sa:

“A taƙaice dai, halayyar da Hajiya Aisha Yan Guru ta nuna na dawo da maɗuɗan kuɗin data tsinta, abune na alfahari ga miliyoyi.”

Inda ya ƙarƙare da

Abin alfahari ne bawai ga yan Zamfara ko Najeriya ba kaɗai, a’a harda musulmin duniya baki ɗaya kwata“. Inji Mallaha.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button