Labarai

Tinubu Yana so yayi shekaru takwas kan Mulki amma ba zai yi nasara ba ~Sheikh Ahmad Gumi.

Spread the love

Fitaccen malamin addinin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya zargi gwamnatin Tinubu da shirin samun shekaru takwas, yana mai cewa ba za su yi nasara ba.

Ko da yake bai ambaci sunan shugaban kasa musamman a cikin faifan bidiyon ba, wanda ya yi ta yaduwa, amma a fili yake cewa malamin yana magana ne akan Tinubu.

Gumi ya kuma ce tikitin tsayawa takaran musulmi da musulmi na jam’iyyar APC na goyon bayan munafukai da mutanen banza.

Ya yi zargin cewa duk da cewa ’yan Arewa ne ke kula da ma’aikatar tsaro, amma rundunar ‘yan sandan na karkashin ‘yan Kudu ne.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button