Labarai

Tinubu zai bayyana majalisar ministocinsa cikin kwanaki 60 – Faleke

Spread the love

Sakataren yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), James Faleke, ya ce shugaba Bola Tinubu zai bayyana mambobin majalisar ministocinsa cikin kwanaki 60.

A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bikin rantsar da Tinubu da Kashim Shettima a matsayin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Faleke, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin a wurin taron, ya ce Tinubu zai bayyana majalisar ministocinsa da wur-wuri.

“Tabbas, a cikin kwanaki 60, abin da doka ta ce ke nan. Zai iya sanar da kowa a kowane lokaci amma na san dole ne ya yi hakan a cikin kwanaki 60, ”in ji shi yana cewa.

A ranar 17 ga watan Maris, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wasu dokoki 16 na gyara kundin tsarin mulkin kasar, ciki har da wanda ya bukaci shugaban kasa da gwamnoni su mika sunayen ministoci ko kwamishinoni da aka zaba cikin kwanaki 60.A shekarar 2015, tafiyar hawainiya da gwamnatin Buhari ta yi, an dora laifin rashin bayyana ministocin da ya yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button