Labarai

Tinubu zai halarci taron G20 a Indiya, domin ganawa da shugabannin duniya

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu zai halarci taron G20 da aka shirya gudanarwa a ranakun 9 da 10 ga watan Satumban 2023 a birnin New Delhi na kasar Indiya. Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan.

A cewar sanarwar daga Mista Ajuri, shugaban kasar na fatan yin amfani da taron wajen jawo hannun jarin kasashen waje kai tsaye (FDI) zuwa Najeriya da kuma bunkasa tattalin arziki da ci gaba.

“Muna mai da hankali kan ayyukan da za su shafi muhimman sassa na tattalin arzikin kasa, da suka hada da bunkasa karafa, samar da wutar lantarki, watsawa da rarrabawa, karfin ginin jiragen ruwa, da sauran masana’antu da dama, wadanda muka san suna da karfin gwuiwa.”

”Mr. Shugaban kasar zai karbi bakuncin babban taron shugabanni, wanda zai kunshi fiye da manyan jami’ai 20 na manyan masana’antu a sassa daban-daban na tattalin arzikin Indiya don tabbatar da cewa mun yi amfani da sha’awarsu na saka hannun jari a kasar.”

A yayin taron, shugaba Tinubu zai gana da shugabannin kasashen Jamus, Brazil, Koriya ta Kudu, da Indiya da dai sauransu domin karfafa huldar diflomasiyya da kuma tattauna bangarorin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da sauran kasashe.

‘G20 babban taro ne ga kasarmu a wannan lokaci kuma za mu tabbatar da cewa mun yi amfani da damar da aka bayar don kawo darajar kasar.”

Game da G20

G20 ita ce taron koli na hadin gwiwar tattalin arziki na kasa da kasa wanda ya kunshi manyan kasashe ashirin mafi girma da ci gaban tattalin arziki na duniya.

An gayyaci shugaban Najeriya a matsayin bako na musamman daga Indiya mai masaukin baki a farkon wannan shekarar yayin da Indiya ke jagorantar kungiyar a halin yanzu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button