Labarai
Tofa: Dayawa Daga Cikin ‘Yan Najeriya Na Cikin Barazanar Shiga Matsanancin Talauci- Inji Buhari.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya nuna damuwarsa akan halin da kuncin rayuwa da talaucin da Jama’a suke ciki, inda yace da yawa daga cikin ‘yan Najeriya a halin yanzu suna rayuwa a matakai daban-daban na talauci.
Ya ce yawan jama’ar da ke kara shiga cikin matsanancin talauci yana kara karuwa.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, Shugaban ya yi magana ne a cikin sakon bidiyo da aka yi rikodin ga wani babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan yadda ake gudanar da zamani, da dabarun kawar da talauci a duk fadin duniya.