Tonon Silili; Ba Yau Ne Young Sheikh Ya Fara Karyar Ilimi Ba – Shehu Rahinat Na’Allah
Wanna hoton da na saka hoton Young Sheikh ne da wasu larabawa tare da mahaifin shi. A jikin hoton an rubuta cewa Young Sheikh yazo na biyu a musabaqar Alqur’ani ta duniya da aka gabatar a lokacin yana Dan shekara uku, an dauki hoton ne Jim kadan bayan kammala Musabaqar. To tambayar da Mike da ita anan itane:
1• Wace Shekara akayi musabaqar ?
2• Wace kasa (Country) akayi musabaqar ?
3• Su wanene alkalan Musabaqar ?
4• A saka mana bidiyon shi koda na minti daya ne lokacin da yake karanta AlQurani a wurin Musabaqar ta duniya.
Don haka irin wannan karyar da yaudara ba yau suka saba yinta ba, kuma suna yi ne don Neman Shahara saidai sun manta cewa: “Hubbuz-zuhour Yam-na’uz-zuhour” wato Neman ka shahara ko ta wane hali yana hana ka shahara din.
Saboda haka ni koda naga hotunan shi wai ya gama degree a sharia banyi mamaki ba.
Na San Young Sheikh lokacin yana Nursery a Makarantar Baban shi mu dauka ya shekara daya a Nursery, Sannan ya shekara Shida a Primary, kunga shekara 7 kenan, to sai ya shiga Secondary mu dauka bai yi Junior ba kawai ya fara ne daga Senior kunga zai shekara uku kenan, totally Shekara goma. To sai ya tafi Jami’a zai yi Degree a Sharia Shekara Hudu, mu dauka su semester hudu suke yi a Shekara kunga zai gama degree dinsa kenan a cikin shekaru biyu, idan muka lissafa gaba daya za muga ya kammala Degree dinsa ne yana Dan Shekara 12, to kuma kar Ku manta akwai wata hira da yayi da Jaridar Aminiya a Shekarar 2022 ya fadi cewa Shekarar shi 8 yanzu kuma muna 2023 ne kunga kenan Shekarar shi 9 a duniya, to Ku dauko lissafin Shekarun karatun shi wato shekara 12 kenan, da kuma shekarun shi a duniya wato Shekara 9 sai kuyi mana alkalanci.
Ae ya kamata idan mutum zai yi karya to yayi wacce hankali zai iya dauka, ta yadda kafin a gano cewa karya yake yi sai an sha wahala.
A karshe, lokaci bai kure masu ba don haka zasu iya gyara duka wadannan karyayyakin domin su Samar masa rayuwa mai inganci nan gaba wacce babu damfara da karya a cikin ta.
.
Sannan duk wanda yake son ya kalli Bidiyon da yace Shekarar shi 8 zai iya shiga wannan link din:
https://www.facebook.com/aminiyatrust/videos/435959231621820/?app=fbl
Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
15th June, 2023