Labarai

Tsadar Abinci ku dai zargin Buhari -Gwamna Badaru

Spread the love

Gwamna Badaru yace da yan Najeriya ku daina zagin buhari kan tsadar abinci Gwamnan jihar Jigawa, Mohammadu Badaru Abubakar ya ce bai kamata ‘yan Nijeriya su dunga zargin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba yana mai cewa matsalar ta samo asali ne tun farko da yan Nijeriya ke shigo da haramtaccen abinci badaru Ya fadi hakan ne yayin da yake yabawa Ministan Sadarwa da Ci Gaban Tattalin Arziki, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, yayin kaddamar da wasu ayyuka fasaha guda 12 da Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC), da NITDA da sauran hukumomin da ke karkashin ma’aikatar. .

Ya ce bai kamata a zargi Buhari kan wahalar da ke faruwa a kasar ba a batun tsadar kayan abinci da sauran kayayyaki a kasuwa ba, yana mai cewa gwamnatocin da suka gabata sun gaza samar da mai da kwatankwacin darajar Naira a kan dala, saboda haka karancin dollar a kasuwar kudi da hauhawar farashin dollars yasa ake cikin wagga matsala idan baku manta ba “‘A cikin shekaru biyar na ƙarshen gwamnatin da ta gabata, ana sayarda da mai a $ 100 kowace ganga, akuma shekara biyar ɗinmu ana sayarwa kan $50 kowace ganga ɗaya. Akalla da rabin albarkatun da Muhammadu Buhari ya samu, mun sami nasarori da yawa. a Ma’aikatar sufurin jirgin sama mun kammala ayyuka 150

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button