Labarai

Tsadar Rayuwa: Naji dadi na Kuma yi matukar farin ciki da yadda Tinubu ya dai-dai Nageriya – Cewar Tsohon Shugaban Nageriya Buhari

Spread the love

Mataimakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana kudurin gwamnati na “aikin tura kayayyakin da ake da su don yaki da rashin tsaro” da kuma tabbatar da “zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.” Ya yi wannan alkawari ne a ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura na jihar Katsina a ranar Asabar. Shettima ya jaddada cewa gwamnatin da shugaban kasa Bola Tinubu ke jagoranta ta dukufa ne wajen ganin ba a bar ta a baya ba a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

A martanin da ya mayar, tsohon shugaban kasa Buhari, ya nuna jin dadinsa da ziyarar Shettima, ya yabawa gwamnati mai ci bisa ayyukan da ta ke yi na daidaita tattalin arziki. Ya kara da cewa, “Na yi matukar farin ciki da yadda suka iya daidaita al’amura tare da ci gaba da nuna damuwa a kan ‘yan Nijeriya, na yi matukar farin ciki da yadda suke gudanar da ayyukansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button