Tsadar shinkafa ya Sanya Magidanta daina cin shinkafa A Kano
Duk da yawaitar kamfanunuwan shinkafa A Kano Amma farashinta Yana hauhawa A kullun A jahar kano
Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano
Mazauna jihar Kano sun koka kan tsadar shinkafa a jihar duk da yawan manoma dake noma ta a fadin jahar
Shinkafa itace madaidaicin abincin A jahar kano Amma sannu a hankali ya zama ba kowwane talaka ne ke iya dafa shinkafa yaci ba saboda tsadar da tayi
‘Yan kasuwa a nasu bangare sun danganta tsadar farashin shinkafa kwanan nan duk da yaduwar kamfanunuwan shinkafar a cikin jihar.
Binciken da mukayi ya nuna cewa yanzu ana sayar madaidaicin buhun na shinkafar gida Mai KG 50 a tsakanin N22, 000 zuwa N24, 000
Yayin da Ake sayar da kwano N16,00
Wani magidanci mazaunin birnin Kano ya koka kan yadda farashin shinkafar yake ta Kara hawa inda yace yanzu shinkafa tana gagarar da yawa daga cikin magidanta, yayi Kira da Gwabnati datayiwa farashin kayan Abinci iyaka (control price)