Tsakanina da barawon dollars waye ya kamata a boye? Wike
Shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a zaben gwamna a jihar Edo, Nyesom Wike, ya ce barazanar da takwaran sa na jam’iyyar All Progressives Congress, Abdullahi Ganduje, na “killace shi” har zaben ya kare, hakan ya tona asirin makircin. Jam’iyyar da ke kan karagar mulki za ta yi amfani da damar jami’an tsaro.Ganduje a ranar Litinin yace jam’iyyar APC za ta wulakanta Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ta hanyar killace Wike. Da yake mayar da martani ranar Talata, Wike ya ce mutumin daya sanya dala a aljihunsa shune ya cancanci a killace shi Ya ce a shedama gwamnan jihar Kano ni ba mai wasa ba ne, yana mai cewa “A tsakanina da mutumin da aka kama da almubazzaranci, wa ya cancanci a boyeshi shi?” Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta tsayar da ranar 19 ga Satumbar don zaben Edo. Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC zai yi adawa da Obaseki, gwamna mai ci kuma dan takarar PDP a zaben.