Tsare magu ba bisa ka’ida ba zai garzawa kotu
Lauayan magu yace bayan dakatar da shi mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Ibrahim Magu, ta hannun lauyan sa, Oluwatosin Ojaomo, ya ce zai gurfana gaban kotu don kalubalantar ci gaba da tsare shi. da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, yakeyi lauayan ya bukaci a saki abokin nasa. Ojaomo, wanda ya zanta da SaharaReporters a yau ranar Laraba a Abuja, ya ce “Mun samu martanin daga IGP din kan beli amma ya ce kwamitin shugaban kasa ne ke tsare shi kuma ya kamata in yi magana da kwamitin.” amma, ni ba zan gamsu da martani ba saboda idan ‘yan sanda sun hana wani belli, to dole ne a dogara ne a kan wani umurni ko dai daga kotu ko daga kwamiti shugaban. “Ba muna yanke hukuncin zuwa kotu ba amma ina so in tabbatar kuma in ga kwafin umarnin tsare wanda ya ba da damar tsare abokin namu” A ranar 6 ga watan Yuli ne wata tawaga ta Ma’aikatar jihohi da ‘yan sanda suka kama shi daga Sashin Binciken Sojoji, a Abuja. a halin yanzu ake masa tambayoyi daga wani kwamiti karkashin jagorancin Ayo Salami, tsohon Shugaban na Kotun daukaka kara domin zargin almubazzarancin gano kudi da kuma rashin nuna gaskiya a gano dukiyar..