Kasuwanci

Tsarin Bada Ranche Na “Nigeria Youth Investment Fund” (NYIF) Sun Fara Tabbatar Da Kudade Ga Wa ‘Yanda Suka Kammala Cika Bayanansu.

Spread the love

….Masu ragista da CAC daga Miliyan Ukku zuwa kasa, wa ‘yanda basu da CAC daga Dubu 500K, zuwa kasa.

A nutsu a karanta da kyau domin a amfana, tare da yiwa al’umma share domin suma su amfana.

A yau Littinin gwamnatin Nijeriya ta fara Approved don baiwa wa ‘yanda suka kammala cika tsarin karbar ranche karkashin tsarin “Nigeria Youth Investment Fund” masu ragista da CAC daga Miliyan Ukku zuwa kasa, wa ‘yanda basu da CAC daga Dubu 500K, zuwa kasa.

Duk Wanda yasan ya kammala cika bayananshi yana shiga Profile din shi lokaci bayan lokaci domin dubawa ko an mishi Approved ko kuma, kowanne lokaci zasu iya yiwa mutum Approved babu tabbacin yaushe zasu yi.

Me Yasa Har Yanzu Miliyoyin Mutane Sun Kasa Samun Dama Domin Su Cika Bayanansu A Manhajar Bayan Suna Daga Cikin Wa Yanda Zaa Baiwa Bashin Ranchen?
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Tun lokacin da aka fara tura wa mutane sakonni domin su cike bayanansu a manhajar daga lokacin network din manhajar ya fara nuna damuwa da matsala saboda yadda Miliyoyin mutane suke ziyartar shafin a kowacce dakika shiyasa har yanzu Miliyoyin Mutane basu iya samun damar saka bayanansu ba, amma a cigaba da gwadawa Inshaallah kowa zai saka, amma hakan yana matukar daukan tsawon lokaci.

Karin Bayani: Yadda Zaka Yi Verified Din Kanka Domin Ka Cike Dukkanin Bayananka
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Idan har kana daga cikin wa yanda zaa a bawa ranchen kuma yayi creating PASSWORD amma har yau Message din Confirmed bai shigo ta Email dinshi ba.

SHIN TA YAYA ZAKA YI CONFIRMED DIN ACCOUNT DINKA DOMIN KA SAMU RANCEN KUDADEN?

Ka ziyarci wannan shafin
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
https://nyif.nmfb.com.ng
Zaka ga wurare guda ukku kamar haka
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
APPLY HERE
LOAN APPLICATION
LOGIN

Saika shiga na Karshe “LOGIN” kana shiga Zaka ga ya nuna maka inda zaka saka BVN number dinka da Password, kada ka saka komai a wajan ka duba kasa zaka ga wa yan nan bayanan kamar a Jere kamar haka
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
Forgot Password? Register! Didn’t Get Verification Token?

Saika shiga “Didn’t Get Verification Token?” Kana shiga zai nuna maka ka saka Gmail dinka sai su turo maka da Message din Confirmed ta Gmail dinka, yana iya daukan tsawon a wanni bai shiga ba, amma da zaran ya shiga sai kayi Sauri ka shiga Link din da suka turo maka kana shiga Zasu nuna maka kamar haka “REGISTRATION SUCCESSFUL” VERIFICATION SUCCESSFULL, YOU CAN NOW LOGIN”.

Amma matukar ya nuna maka “Your Verification Has Been Fail” to dole saika sake komawa ka sake tura Gmail dinka sun sake turo maka da Confirmation Code din, saboda basu son ya dade baka yi Confirmed ba, matukar sun turo maka.

Kana kammala hakan sai ka sake Komawa wajan “LOGIN” ka saka BVN number dinka da PASSWORD din da ka saka a lokacin da kayi Creating account din tun farko.

Bayan ka saka ya bude maka zasu fara maka tambayoyi kana amsawa, inda zasu fara da tambayanka shin kana da ragista da CAC ko kuma Individual ne kake gudanar da kasuwancin naka…

Matukar baka da ragista da Hukumar CAC kada ka saka kana da ita, saboda da zaran ka saka kana da ita, akwai inda suke bukatan ka saka musu da Dukkannin Information din ragistar kamfanin naka da hoton ragistar da TIN number, idan baka dasu to tabbas kayi asarar damar samun rancen kudaden.

Haka zalika duk wanda yake da ragista da CAC matukar ba shida “TIN” number kada ya kuskura ya saka musu cewa yana da ragista, kwanda kawai ya cika a individual.

MENENE “TIN” NUMBER?

“TIN” shine “Tax Identity Number” ana Mallakar TIN number ne ga wa yanda suke da ragista da CAC, zasu je Hukumar dake karbar REVENUE ta kasa mai suna “Federal Inland Revenue Service” “FIRS” ko kuma wadda take karkashin jaha a basu kuma kyauta ne, dole sai kamfani, kungiya suna dashi Kafun su bude account a Banki.

NAWA KOWA ZAI IYA NEMAN RANCE A TSARIN NYIF?

An yi chanje chanje a tsarin “Nigeria Youth Investment Fund” (NYIF) a wajan bada ranche.

Duk wanda yake da ragista da CAC zasu bashi rance daga Miliyan Ukku zuwa kasa.

Duk Wanda ba shida ragista da CAC zasu bashi rance daga 500,000 zuwa kasa.

GARGADI:
Kada a Cika abunda ya wuce haka, matukar mutum yana son su bashi rancen.

DAME DAME SUKE BUKATA?

Da farko dai suna bukatan “INDIGINE LETTER” takaddar shaidar kai cikakken dan Jihar da kake zaune.

Sai sauran bayananka na Banki da ire iren kasuwancin ka, amma yana da kyau ka nemi Wanda ya iya turanci mai kyau domin cike maka sauran bayanan yadda ya kamata.

YAUSHE KUDIN ZAI SHIGA ACCOUNT DIN MUTUM?

Duk Wanda ya kammala cike dukkannin abubuwan da ake bukata zasu nuna mishi
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

“YOUR LOAN APPLICATION HAS BEEN SUBMITTED FOR REVIEW AND APPROVAL”

Da zaran sun nuna maka haka to tabbas ka kammala shiga sahun jerin Mutanen da zasu iya samun rancen adadin Kudaden da ka nema Inshaallah, sai a cigaba da Addu’a kuma a na shiga Manhajar lokaci bayan lokaci domin ganin anyi APPROVED dinka ko ba’a yi ba.

Duk halinda ake ciki da zaran ka Shiga zaka gani, da zaran anyi APPROVED dinka bada dadewa ba, zaka ga kudinka sun shiga DIRECT Account dib bankinka babu bata lokaci.

MENENE MATSALAR WA ‘YANDA SUKA CIKA TUN SHEKARAR DA TA GABATA, AMMA BASU SHIGA SAHUN WA ‘YANDA ZA’A BAWA RANCEN A YANZU BA?

Miliyoyin mutane ne suka nemi ranchen amma sai aka zabo wasu daga ciki tun a shekarar da ta gabata aka fara basu ranchen, shine yanzu ma suka sace zakulo wasu daga cikin wa yanda suka cika tun shekarar da ta gabata zasu bawa, suma wa yanda baa neme suba nan gaba kadan Inshaallah zasu nemi su.

DUK WANDA BAI YI APPLY BA YA KAMATA YA SHIGA YAYI APPLY A YANZU
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://nyif.nmfb.com.ng

Wa yanda suka yi APPLY a cikin wannan shekarar su kwantar da hankalinsu suma zaa nemi su nan bada dadewa ba Inshaallah.

Allah Yasa Mu Amfana. Amin

Rubutawa✍️✍️✍️
Comr Abba Sani Pantami
National Chairman
Arewa Media Writers

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button