Tsaro
Tsaro: Dan majalisar Ya Yi Abin Da Gwamnoni Da Yawa Suka Kasa.
Dan majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabun Bosso da Paikoro a Zauren Majalisar Tarayya Hon. Shehu Barwa Beji Ya Rabawa Mashina Kirar Bajaj guda 20 ga Yan Banga Musu Sintiri a Yankunan.
Beji yace Ya raba Mashinan ne da Zummar Inganta Tsaro a Yankin da yake Wakilta, Sannan Ya Musu Fatan Alheri da Samun Nasara Kan Masu Tada Kayar baya a Yankin.
Beji ya yi kira ga Al’ummar Yankin da Su Hada Hannu da Jami’an Yan Bangan da Su yaki ta’addanci a yankin dama Jaha baki daya.