TSARO: Ya Kamata ‘Yan Nijeriya Su Tsaya ga Adu’a; domin Addu’a ce Zata Cece Mu Daga Rashin Tsaron Kasar nan —Cewar Shugaban Kasa Remi Tinubu
Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta bukaci ‘yan kasar da su kara zage damtse wajen neman taimakon Allah kan matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.
Tsohuwar ‘yar majalisar ta bayyana haka ne a shafinta na X (Twitter) a yau ranar Litinin yayin da take mayar da martani kan ceto wasu ‘yan uwa mata biyar na gidan Al-Kadriyar da aka yi garkuwa da su a unguwar Bwari da ke Abuja.
Uwargidan shugaban kasar ta bayyana addu’o’in a matsayin mafita ga matsalar sace-sacen jama’a da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane ke yi a fadin kasar nan.
A cewar uwargidan shugaban kasar, ya kamata a yi la’akari da addu’o’i a matsayin makamin farko da Najeriya za ta iya magance tashe-tashen hankula, kuma bai kamata a yi amfani da hakan da wasa ba daga yanzu.
Ta ce, “Ina taya ‘yan uwa da abokan arziki da ‘yan Nijeriya murnar dawowar ‘yan uwa mata na Al-Kadriyar lafiya. Addu’a tana aiki kuma ina mika godiya ga daukacin ‘yan Najeriya musamman iyaye mata da suka yi addu’ar Allah ya dawo mana da ‘yan uwa Al-kadriyar. Kada mu fasa tuba a cikin addu’o’inmu.