Ƙungiyar Boko Haram na raba dubu ashirin-ashirin kyauta ga mutane a garin Geidam.

Bayanai sun fara yawo dangane da yadda ƴan ta’addan Boko Haram ɓangaren ISWAP suka fara rabon dubu ashirin-ashirin ga magidanta a garin Geidam ta Jihar Yobe.

Masana akan al’amuran yau da kullum sunyi sharhin cewa rabon kuɗaɗen da yan ta’addan suka fara, yana da babbar alaƙa da yunƙurin ƴan ta’addan wajen janyo hankalin al’umma domin shiga ƙungiyar mai iƙirarin jihadi.

Kamar dai yadda aka sani, ƙungiyar ta ƴan ta’addan sun mamaye garin na Geidam ne tun ranar Juma’ar data gabata bayan mummunan harin da suka kai cikin garin. Hakan ne ma yasa suka riƙe wasu daga cikin al’ummar garin domin zama garkuwa garesu, musamman a yunƙurin da suke na hana jami’an tsaro fatattakar su daga garin na Geidam.

Jaridar Daily Trust ta bayyyana yadda wasu daga cikin mutanen garin na Geidam suka tsere zuwa garuruwan Damaturu, Dapchi, Babban Gida da Gashua sakamakon harin na kwana-kwanan nan.

Ɗaya daga cikin mazauna garin ya tabbatarwa da manema labaru cewa har kawo yanzu, ragowar mutanen da suke zaune a cikin garin suna cigaba da karɓar dubu ashirin-ashirin kyauta daga ƙungiyar ta Boko Haram a matsayin tallafin azumi.

Ya kuma ƙara da cewa, mafi akasarin mutanen garin suna karɓar kuɗaɗen ne akan dole; saboda gudun azabtarwar ƴan ta’addan.

A gefe guda kuma; wani ƙwararre a fannin tsaro mai suna Salihu Bukhari, ya bayyana cewa dabarun nunawa mutane soyayya da ƙungiyar ta ISWAP keyi, shine silar ƙara bunƙasar su fiye da ɓangaren na Boko Haram da Abubakar Shekau yake jagoranta.

A ƙarshe ya ƙara da cewa ya zama wajibi ga gwamnati tayi duk mai yiwuwa wajen fatattakar yan ta’addan daga cikin garin na Geidam; domin hana su ƙara samun damar juyar da hankalin sauran mutanen garin wajen karɓar mummunar aƙidar ta ta’addanci.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *