Ƴan bindiga sun hakkala aƙalla mutane 50 a ƙauyukan Zamfara.

Mutane aƙalla 50 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin bazata da ƴan bindiga suka kai ƙauyuka guda shida dake ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Shedun gani da ido sun tabbatarwa da manema labarai cewa; tun satin daya gabata ƴan bindigar suka fara kai hari a yankunan, yayin kuma daga bisani suka ƙara shammatar mutanen ƙauyukan jiya Laraba tare da yin nasarar hallaka aƙalla mutane 50 a tsakanin kauyukan guda shida.

Har’ilayau; kawo yanzu ba’a san wurin da ɗaruruwan mazauna yankunan da iftila’in ya shafa waɗanda suka haɗa mata da ƙananan yara suka shiga ba. “Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa”.

Yayinda gidaje haɗe da rumfunan kasuwanci da dama suka salwanta sakamakon harin.

Daga Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *