Ƴan fashi sun hallaka Limami da wani bawan Allah a Zamfara

A ranar Litinin ne wasu ƴan bindiga da ake zargin ya fashi ne, suka afkawa kauyen Kwangwami dake ƙaramar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara, inda suka hallaka limamin garin wato Alhaji Liman Auwalu, wanda shine limamin masallacin Kwangwami haɗe da wani bawan Allah wanda tsautsayi yahau kansa.

Kamar yadda yan ƙauyen suka zayyanawa manema labarai, yan fashin sun lalata amfanin gona mai yawan gaske, sannan suka gudu da shanu haɗe da abubuwa masu matuƙar tsada na yan ƙauyen.Kamar yadda Ibrahim Kwangwami ya bayyanawa manema labarai, yace yan bindigar sun shigo garin ne akan babura ɗauke da makamai. Suna da yawan gaske, sannan angansu suna harbin kan mai uwa da wabi.

Majiyarmu ta samu bayanin cewa; Alhaji Liman Auwalu ya gamu da wani harsashi ne yayin da ɗayan mutumin da ake wa laƙabi da suna Hamisu Bako yace ga garinku nan.

SP Mohammed Shehu shine kakakin hukumar ƴan sandan jihar Zamfara, kuma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bada tabbacin cewa yan sandan sun ɗau matakin kare aukuwar haka nan gaba, kuma ya bada tabbacin cewa ana nan ana ƙoƙarin ƙwamushe masu laifin.Shehu ya ƙara da cewa, zaman dar dar da akeyi, ya ragu domim zaman lafiya ya dawo a yankin.

Harin dai yana zuwa ne ƙasa da awa ashirin da huɗu bayan gwamnatin jihar Zamfara da ƴan sandan jihar sun musanta kashe mutane ashirin da uku a kasuwar ɗan sadau can cikin ƙaramar hukumar Maru ta jihar.

Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *