Ƴan ta’adda sun sace basarake da wasu mutane 20 a Katsina.

Wasu ƴan ta’adda ɗauke da makamai sun kai hari ƙauyukan ƙaramar hukumar Sabuwa da ke jihar Katsina, a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, inda suka yi awon gaba da wani mai gari da wasu mutane kusan 20.

Ƙauyuka uku- Gamji, Ungwar Mato da wani ƙauye a karamar hukumar Faskari na jihar ƴan ta’addan sun kai musu hari wanda suka kwashe kimanin awanni uku suna aiki, inji rahoton Human Angle.

Shaidun gani da ido sun ce maharan waɗanda aka sani da ƴan fashi daga yankin sun taka zuwa kauyen Gamji, saɓanin hare-haren da suke a baya inda suka zo kan babura.

Wani daga cikin mazauna garin wanda bai so a ambaci sunansa ba saboda tsaron lafiyarsa ya ce ya tsere ne cikin daji lokacin da gungun masu garkuwar suka zo.

Ya ce ƴan bindigar sun afka wa kauyen da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Talata inda suka buɗe wuta a kan mazauna garin, suka yi awon gaba da hakimin da wasu mutane 25.

“Babu wanda zai iya faɗin takamaiman adadin mutanen da suka sace; duk mun san cewa sun sace Hakimin ƙauyen da wasu da yawa, ”inji shi.

“Mun bincika daga gida zuwa gida a safiyar yau kuma mun gano cewa mutanenmu 25 suna hannunsu a yanzu,” in ji wani mazaunin garin wanda ya yi magana ba tare da ambaci sunansa ba saboda dalilan tsaro.

“Sun zo ne kamar mutanen da suka yi kaura daga wani wuri, ɗauke da makamai ɗauke da fuskokinsu.”

“Wasu ƙannena biyu suna hannunsu a yanzu; ɗaya daga cikinsu ɗalibin karatun lauya ne a makarantar koyon aikin lauya ta Yenagoa yayin da ɗayan kuma ya kammala karatun aikin injiniya a Jami’ar Bayero ta Kano, ”ya ci gaba

Ya ce babu jami’an tsaro a kusa da ƙauyen yayin harin yana mai cewa ƙauyen yana tsakanin Ɗandume da ƙaramar hukumar Sabuwa.

Wani wanda abin ya faru a gaban idanunsa ya ba da labarin cewa ƴan ta’addar sun kwashe kimanin awanni uku a ƙauyen.

“Sun kasance a kauyen daga ƙarfe 10 na dare har zuwa 1 na safe kuma ba su tafi ba saboda babu matsin lamba daga jami’an tsaro,” in ji shi.

“Mun kai rahoton lamarin zuwa shingen binciken sojoji amma ba su amsa ba sam.”

Ƴan bindigar, a cewar majiyoyi a Unguwar Mato sun yi garkuwa da mutane uku ciki har da mata biyu kuma suka yi awon gaba da kayan abinci da magunguna.

Wannan ya faru ne sa’o’i kadan bayan da kungiyar ta mamaye ƙauyen Bilbis na ƙaramar hukumar Faskari inda ta kashe mutane huɗu, ta raunata wasu mutane da ba a bayyana adadinsu ba sannan suka kwashe dabbobinsu, in ji wata majiya.

Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yamma da ke fuskantar munanan hare-haren ƴan fashi duk da ikirarin fadar shugaban ƙasa da gwamnatin jihar cewa lamarin yana ƙarkashin iko.

Idan za a iya tunawa, Sojojin Najeriya sun ƙaddamar da atisayen Sahel da kuma Super Camp a ƙaramar Hukumar Faskari da ke jihar don ganin an sake gano ayyukan ƙungiyoyin masu aiki da muggan makamai a jihohin Katsina da Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published.