Ɗan Majalisa Ya Shiga Daji Da Kansa Ya Ceto ‘Yan Mazabarsa Da ‘Yan Bindiga Suka Sace.

Hon Sa’idu Baba Ahmad, dan majalisar Kwara mai wakiltan mazabar Gwanabe-Danmi- Adera ta yankin karamar hukumar Kaiama kuma mamba a kungiyan sintiri na Miyetti Allah, ya jagoranci wata tawagar yan sintiri da jami’an tsaro zuwa daji.

A cikin haka, sun yi nasarar kubutar da wasu mutane 13 yan mazabarsa wadanda yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Har ila yau tawagar sun kuma yi nasarar halaka yan bindiga hudu a yayin musayar wuta da suka yi dasu.

Dan majalisar ya bayyana cewa sun kwashe tsawon kwanaki suna aikin sintiri a cikin jejin Old Oyo National Park kafin su tarar da yan bindigar, kamar yadda sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

A cewarsa, sun shafe kwanaki uku suna shiga jeji suna farautar yan ta’addan inda daga baya suka yi nasarar ceto mutane 13 da suka yi garkuwa da su.

Sa’idu ya kara da cewa babu mutum ko guda da ya ji rauni a cikin wadanda suka kubutar, dukkansu suna cikin koshin lafiya, sannan sun kai wadanda suka nuna alamar galabaita asibiti ana duba su.

Ya ce: ”Mun samu gawawwaki hudu a cikin ‘yan bindigar, kana mun kwato bindigogi ƙirar AK 47 da kwanson harsasai shida da harsasai guda 67.”

Sai dai ya ce basu yi nasarar kama sauran ‘yan bindigar ba wanda adadinsu su tara ne, amma kuma biyu daga cikinsu sun tsere da raunukan harsasai.

Ya ce sun samu wannan nasara ne ta hanyar gangamin hadin gwiwa da ‘yan sintiri na Fulani da Yarbawa, sojoji da yan sanda har da shugaban karamar hukumar Kayama.

”Sai da muka kasu gida biyu da tawagarmu da ta jami’an tsaro, amma tawagarmu ce ta yi arangama da su.

”Muhimmancin wannan sintirin da muka yi shi ne muddin muka bari suka yi kaka gida a wajen za su hana mutanenmu walwala, amma Alhamdlillahi da muka tarwatsa su yanzu za a samu zaman lafiya,” a cewar shi.

Dan majlisar ya bayyana cewa tun dama chan shi dan kungiyar Miyetti Allah ta jihar Kwara ne tun kafin ya san zai zama dan majalisa.

Ya kuma rike muƙamin sakataren kungiyar har na tsawon shekara takwas, yana kuma gudanar da ayyukan sintiri a cikin kungiyar.

Daga karshe ya ce sun mika gawawwakin ‘yan bindigar hudu da suka rasa rayukansu a rangaramar ga rundunar ƴan sandan Najeriya

Daga Amir sufi

Leave a Reply

Your email address will not be published.