Tsaro

A cikin kwanaki uku, ‘yan bindiga sun kashe mutane da yawa, sun sace sama da 50 a cikin al’ummar Sokoto

Spread the love

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun kashe mazauna gari da yawa tare da yin garkuwa da wasu sama da 50 a yayin hare-haren da suka kai kan al’umomin Goronyo, Gada da Sabon Birni na jihar Sokoto.

Lukman Iliyasu, mazaunin Sabon Birni, ya ce an kai hare-haren ne tsakanin ranakun Litinin zuwa Laraba.

Iliyasu ya ce ‘yan bindigar sun mamaye al’ummomin da dama, inda suka rika harbe-harbe a kai-a kai, kuma sun yi sanadiyyar jikkata wasu da dama.

“Harin ya fara ne daga ranar Litinin zuwa Laraba. Kauyukan da abin ya shafa suna cikin kananan hukumomin Goronyo, Gada da Sabon Birni.”

“Kauyukan da aka kai wa hari jiya a Sabon Birni su ne Dan Gari inda aka kashe mutum bakwai aka yi garkuwa da mutane da dama, a Kurawa an kashe mutum biyu sannan aka yi awon gaba da wasu da dama, sai kauyen Gumozo, an kashe mazauna garin uku, an kuma yi garkuwa da wasu da dama.

“Suna shirin mamaye kauyen Gatawa ne sai jami’an tsaro suka ritsa su, sai na samu labarin an kashe wasu ‘yan bindigar a cikin lamarin.

“’Yan bindigar sun kashe mutane da dama tare da kwashe mutane sama da 50 daga wasu kauyuka. Kun san yadda suke aiki, sun mamaye al’ummomi daban-daban a ranaku daban-daban. Sun dade suna kai hari Sabon Birni. Har ma sun sanya wa al’ummarmu harajin zaman lafiya na dole.

“Wannan ita ce shekara ta biyu da aka dora mu kan tilas biyan kudin zaman lafiya. Sun ce ba za su bari manoman mu su je gonaki su yi noma ko girbi kayan abinci ba.

“A shekarar da ta gabata sun sanya Naira miliyan uku a Sabon Birni saboda yawan al’ummarmu amma Naira miliyan 1.5 kawai muke iya biya. A bana an nemi mu biya Naira miliyan 2 saboda an rage yawan jama’a domin an kashe mutane da dama wasu da dama kuma sun rasa muhallansu amma Naira miliyan daya kawai muka biya.”

Dan majalisa mai wakiltar Gada ta Gabas a majalisar dokokin Sokoto, Kabir Dauda, ​​a wata hira da gidan rediyon Vision FM a jihar, ya ce a cikin mutane 50 da aka sace akwai mata da kananan yara, inda ya ce har yanzu suna hannunsu.

Dauda ya ce barayin sun bukaci Naira miliyan 5 domin a sako kowane mutum daya.

Ya kara da cewa, “Watanni biyu da suka gabata, lamarin tsaro ya ragu amma a halin yanzu, lamarin ya kara tsananta fiye da yadda yake a da.”

“A halin yanzu, muna da mazauna sama da 50 da ‘yan bindigar ke tsare da su. A ci gaba da kai harin, wasu mutane sun samu raunuka daga harbin bindiga.

“Wasu daga cikin wadanda suka jikkata suna asibitin kwararru, wasu suna Goronyo, wasu kuma suna Gada.

“Wadancan wasu kauyuka ne da suka mamaye. Abubuwan da suka faru duk sun faru a cikin mako guda. Sun yi ta zuwa kowace rana har tsawon kwanaki uku a jere. Duk waɗannan sun faru a makon da ya gabata.

“Sun mamaye Basana, sun kashe wasu sun yi awon gaba da wasu, sun kuma kai hari Tsitse, Balakozo, sun dauki yara da wasu da dama, suka mamaye Karangiya suka yi awon gaba da mutane uku sannan suka harbe wasu da dama. Har ila yau, sun kai hari Garin Hashimu, sun kashe wasu mazauna garin sannan kuma sun tafi tare da mutane da dama.

“Gaba ɗaya, mutanen da suka yi garkuwa da su, waɗanda zan iya tabbatarwa, mutane 50 ne daga ƙauyuka daban-daban.

“A halin yanzu, yawancin mazauna ciki har da mata da yara, suna tare da ‘yan bindigar. Ba mu da isassun jami’an tsaro da za su taimaka wa mazauna wurin saboda har yanzu lamarin na ci gaba da yaduwa.”

Dan majalisar ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan, yana mai cewa “babu wani abu da aka yi domin kare wadannan mutane”.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sanda a Sakkwato Sanusi Abubakar ya ci tura domin bai amsa kira ko sako ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button