Tsaro
A Kowace Rana Al-ummar Najeriya Na Kara Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali ~ Gwamnatin Najeriya


Gwamnatin tarayya tace Najeriya na samun zaman lafiya da aminci kowace rana tare da nasarori a yakin da take da Boko Haram/ISWAP, yan bindiga da sauran ayyukan ta’addanci.
Ministan yada labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammed, ne ya fadi haka a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Yace dakarun tsaro a Najeriya sun zafafa yaki da yan bindiga kuma suka jefa su cikin halin gudun buya yayin da kullum ake kara tarwatsa sansanonin su zaman lafiya kullum karuwa yake yi a fadin kasar.
Shin ko kun yadda da wannan zancen?
Daga Comr Abba Sani Pantami