Akwai manyan mutane da ƴan kasuwa waɗanda suke da hannu wajen taimakawa ƴan ta’adda a Nigeria ~ Malami

Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa akwai mutane waɗanda suke ɗaukar nauyin ta’addanci a Nigeria.

Ministan ya faɗi hakan ne jiya Juma’a, kamar yadda bincike ya tabbatar da akwai manyan mutane da ƴan kasuwa waɗanda a gefe guda suke ɗaukar nauyin ta’addancin da yake faruwa a Nigeria.

Ya bayyana cewa tuni bincike yake cigaba da gudana akan mutanen da ake zargi, kuma nan bada jimawa ba za’a gurfanar dasu a gaban shari’a.

Malami ya bayyana hakan ne yayin wata fira da ƴan Jarida a fadar Shugaban ƙasa suka yi dashi jiya Juma’a; yadda kuma ya tabbatar da cewa wannan al’amari ya fallasa ne bayan wasu ƴan asalin Nigeri mazauna UAE da ake zargi suna da hannu dumu-dumu musamman wajen tallafawa ƴan ta’addan Boko Haram.

Hakan ya biyo bayan zafafan hare-haren da ƴan ta’addan Boko Haram suke cigaba da kaiwa a wasu sassa da yankunan Nigeria.

Idan ba’a manta ba dai a ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 2020 Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton yadda wata kotu a birnin Abu Dhabi na United Arab Emirates ta tabbatar da damƙe wasu mutum shida da zargin tallafawa ƙungiyar Boko Haram ta fannoni daban-daban.

Har’ilayau Malami ya ƙara da cewa Gwamnatin Nigeria zata ruɓanya ƙoƙarin binciken ƙwaƙwaf domin cigaba da bankaɗo duk masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Nigeria.

Ina mutuƙar farin ciki yadda wannan bincike yake gudana, kuma hakan zai bamu damar gano duk wani ɓoyayyen al’amari game da taɓarɓarewar tsaro a faɗin Nigeria.

A ƙarshe ya bayyana cewa a halin yanzu ba za’a iya ƙayyade adadin mutanen da ake zargi da ɗaukar nauyin ƴan ta’addan na Boko Haram a Nigeria ba har sai binciken da ake gudanarwa ya kammala.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *