Tsaro

Allah ya kaddara ku wahala, ‘yan fashi sun firgita ku – Gwamna Bagudu ya fadawa ‘yan gudun hijirar Kebbi

Spread the love

“Ku yi hakuri da halin da ake ciki kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya kaddara,” in ji Gwamna Atiku Bagudu.

Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi ya gargadi ‘yan gudun hijira a Mahuta da Isgogo na kananan hukumomin Fakai da Zuru da kada su koma gida har sai ‘yan bindiga sun daina addabar jihar. Ya ce wahalar da suka sha Allah ya kaddara.

Mista Bagudu ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa sansanin ‘yan gudun hijira da ke makarantar Government Day Secondary School, Mahuta da Model Primary School, Isgogo, a Masarautar Zuru a ranar Juma’a.

Ya jajanta wa wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su tare da jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a lokacin da lamarin ya faru.

“Na zo nan ne domin ganin ku tare da manyan mutane da jami’an kananan hukumomi domin jajanta muku. Ku yi hakuri da halin da ake ciki kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya kaddara,” inji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa tuni ya bayar da umarnin a samar da kayan agaji da kuma daukar matakan tsaro a dukkan wuraren da abin ya shafa.

Mista Bagudu ya kara da cewa, “Gwamnati za ta taimaka maku. Za ku zauna a nan har sai an sami lafiya ku koma. Muna daukar karin matakai don kare rayukanku da dukiyoyinku.”

Gwamnan, ya yi gargadin illar yada jita-jita da labaran karya, wanda ya ce za su iya kara sanya tsoro a cikin mazauna jihar.

Mista Bagudu ya kuma ziyarci fadar masarautar Mahuta, Muhammad Hudu, tare da mika ta’aziyya ga shugaban al’ummar. Ya kuma yi taro da shugabannin LG, kansiloli da sauran masu ruwa da tsaki.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button