Baiwar Allah kenan: Yadda akayi wata matar masu garkuwa da mutane ta kuɓutar da waɗanda aka sace Musulmai guda 11 a Katsina.

A ƙalla mutane goma sha ɗaya ne suka shaƙi iskar ƴanci gamida kuɓuta daga ƙangin masu garkuwa da mutane biyo bayan sace mutanen da aka yi a masallacin Jibiya dake jihar Katsina.

Masu ibadar dai, an sace sune a ranar litinin, a bayan garin Jibiya lokacin da suke gudanar da Sallah Cikin dare.

Wani mazaunin yankin, ya shaidawa gidan talabijin na Channels TV cewar, mutanen anga sun dawo gida ne ranar laraba a can ƙaramar hukumar Zurmi da yammaci sakaliya.

Kamar yadda shaidar gani da ido ya tabbatar, ya shaidawa majiyarmu cewa, guduwar mutanen ta samo asali ne sakamakon wata matar masu garkuwa da mutanen data tausaya musu sannan ta kwance , kuma ta nuna musu hanya tace suyi ta gudu.

Inda cikin ikon Allah, a cikin waɗanda suka samu kuɓuta aka samu maza takwas, mata uku.

Mace ɗaya ce Allah baisa ta samu damar kuɓuta ba, wannan kuwa ba wata bace, face wata mata mai jego wadda ta kasa gudu saboda ƙafafuwanta duk sun kumbura saboda jego.

Dalilin haka ne yasa masu garkuwa da ita yanzu haka suke buƙatar biyan kuɗin fansa har na naira miliyan goma kafin su sake ta.

Hukumar ƴan sanda ta jihar suma sun tabbatar da faruwar lamarin duk da cewa kiran da akayiwa mai magana da yawun hukumar na jihar bai ɗauki kiran ba balle ya tofa albarkacin bakinsa akan lamarin ba.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *