Bata gari a Akwa Ibom sun cinnawa Ofishin Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) wuta

Wasu fusatattun mutane sun cinnawa Ofishin Hukumar Zaɓe ta ƙasa wuta a ƙaramar hukumar Essien Udim dake jihar Akwa Ibom.

Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da ilmantar da masu zaɓe, Festus Okoye ne ya tabbatar da faruwan hakan a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar.

Okoye ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, 2 ga Mayu 2021. Amma masu gadin wajen sun samu kuɓuta ba tare da ko ƙwarzane ba, sai dai gine gine-gine dake sansanin ofishin an lalata shi matuƙa, kamar yadda Okoye ya tabbatar.

“Kayayyakin da aka lalata sun haɗa da akwatunan zaɓe 345, ƙananan ƙuri’u 135, wayoyi masu ƙarfi, tankunan ruwa da kayan ofis.”Ƴan sanda, wadanda su ma suke ta fama da hare-hare kan cibiyoyinsu da ma’aikatansu a yankin, suna sane da faruwar lamarin kuma sun fara bincike,” in ji Okoye

Ya ƙara tunawa da cewa ko a gab da zaben 2019, an ƙone sabon ofishin ƙaramar hukumar ta INEC a Ibesikpo Asutan, yayin da aka ƙara jefa wasu ofisoshi biyu a ƙananan hukumomin Mkpat Enin da Gabashin Obolo.

Ya ce, “Harin baya-bayan nan da aka kai wa cibiyarmu bayan mun kammala ƙidaya kayayyakin zaɓe a duk faɗin ƙasar cikin shirin tunkarar babban zaɓe na 2023 abin damuwa ne. Idan ba a kula ba, waɗannan hare-hare na iya haifar da koma baya ga shirye-shiryen hukumar, gami da ci gaba da daƙile ƙoƙarin da muke na maida takaddun zaɓe zuwa rukunin Zabe, aikin ci gaba da Rajistar Masu Zabe (CVR) mai zuwa da gudanar da zaben shi kansa”.

“Duk da haka, hukumar tana son tabbatar wa

ƴan Najeriya cewa ba za mui bar ƙasa a gwuiwa ba don murmurewa daga abin da ya faru a jihar Akwa Ibom ba, kuma zamu cigaba da shirya wa dukkan ayyukan zaɓen da suke tunkararmu”.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *