Bello Matawalle ya bayar da umarnin harbi ga duk wanda aka kama da bindiga ko makamin yaƙi a Jihar Zamfara.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dr Bello Matawalle ya baiwa Jami’an tsaro dake faɗin Jihar umarnin harbi ga duk mutumin da aka kama da bindiga idan har ba Jami’in tsaro ba ne.

Gwamnan ya bayarda wannan umarni ne sa’o’i kaɗan da suka gabata cikin wani saƙo na musamman da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Matawalle ya bayyana cewa Jami’an tsaro kawai doka ta baiwa damar mallakar bindiga ko makamin yaƙi “Saboda haka duk mutumin da aka kama da bindiga a harbe shi “kamar yadda fadar Shugaban ƙasa ta bayarda umarni a kwanakin baya”.

A ƙarshe ya tabbatarda cewa Gwamnatinsa zata cigaba da baiwa ƴan Sanda, Sojoji da dukkan Jami’an tsaro goyon baya domin cigaba da ayyukan kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu a Jihar Zamfara dama ƙasa baki ɗaya.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *