Boko Haram: Jam’iyyar PDP ta Ƙasa ta buƙaci Buhari ya sutale Pantami.

A ranar lahadin nan ne babbar jam’iyyar adawa da ƙasa tayi kira da babbar murya ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari akan buƙatar ganin ya cire ministan sadarwa na ƙasa Isa Pantami.PDP tayi kiran ne abisa bayan an alaƙanta babban malamin da alaƙa da ƙungiyar Taliban da Al-Qaeda, wanda tuni ministan ya fito ya ƙaryata zancen.

Sai dai duk da ƙaryata zancen da yayi, jam’iyyar PDP tayi kira da cewar, yakamata shugaban ƙasa ya dauki mataki akan lamarin na Pantami, tunda magana ce mai matukar jan hankali da take buƙatar kulawa ta musamman.

A wani jerin saƙon ni da tsohuwar jam’iyyar da tayi mulkin Najeriya ta fitar, tayi kira da babbar murya ga hukumar tsaro ta farin kaya dasu gayyaci Pantami domin amsa tambaya.A cewar bayanan da PDP ta saki:

Jam’iyyar mu na buƙatar Shugaba @MBuhari ya gaggauta sallamar ministan, saboda la’akari da yadda batun ke cikin ɓukata adau mataki da gaggawa. “Tsarin jam’iyyar mu an tsara shi ne a kan damuwar da ake da ita a cikin al’umma da kuma a dandalin ƙasa da ƙasa na yiwuwar sasantawa…….., wanda ke da damar samun bayanan gwamnati da bayanai, baya ga bayanan dukkan mutane ciki har da manyan mutane a cikin bangarorin gwamnati da masu zaman kansu gami da al’adun gargajiya da na addini.

“@OfficialPDPNig ta damu matuƙa game da zargin da ake yi a ƙasa akan cewa minista yayi kafar ungulu ga aikin rajistar NIN ta hanyar ba da damar yin rajistar wa baƙi ƴan kama wuri zauna domin sun mamaye mu daga wasu kasashen a matsayin ƴan ƙasa. “Jam’iyyar mu tana kira ga DSS da ta binciki zargin, wanda ya haifar da fargaba, musamman ganin ƙaruwar ayyukan‘ yan fashi da sauran ayyukan ‘yan ta’adda a kasarmu.

“@OfficialPDPNig tana kira ga ‘yan Najeriya da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da kula da muhallinsu, kuma kada su jinkirta wajen samar da bayanai masu amfani ga hukumomin tsaronmu don amfanin kasarmu.” Duk inji PDP.

Abin jira agani shine wani mataki shugaban ƙasa zai dauka gameda wannan batun.

Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *