Boko Haram sun kai hari karamar hukumar Monguno ta Borno – Majiyoyi

‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari karamar hukumar Monguno ta jihar Borno a ranar Laraba, an jiyo karar harbe-harbe da fashewar abubuwa, wanda ya sa dubunnan mazauna yankin da ‘Yan Gudun Hijira (IDPs) suka tsorata.

Wannan na zuwa ne ‘yan awanni kadan bayan an gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan zaman lafiya a Maiduguri tare da gwamna Babagana Umara Zulum da kwamishinan Jiha na Noma Hon. Mustapha Baba Shehuri da sauran manyan shugabannin gargajiya da na addini.

Monguno yana arewa mai nisan kilomita 70 daga Maiduguri babban birnin jihar wanda ya karbi dubban ‘yan gudun hijirar da galibi daga yankunan Kukawa, Dikwa da Marte suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published.