Buhari ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta kubutar da Ɗaliban makarantar Islamiyya 200 da aka sace a jihar Neja nan take.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin tsaro da na leken asiri da su hanzarta yunkurinsu na kubutar da yara 200 da aka sace daga makarantar Islamiyya a jihar Neja.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana haka a ranar Litinin a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Gaggauta daukar mataki game da sakin yaran makaranta, Shugaba Buhari ya bukaci jami’an tsaro.’

Ya ce Shugaba Buhari ya karbi bayani a kan sabon abin da ya faru na satar makaranta kuma ya yi Allah wadai da shi.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tuhumi jami’an tsaro da na leken asirin kasar da su hanzarta kokarin ganin an dawo da yara 200 da aka sace daga makarantar Islamiyya a jihar Neja,” sanarwar ta karanta a wani bangare.

Ya kara da cewa Shugaba Buhari ya bukaci dukkanin hukumomin da ke cikin aikin ceton da su yi iya kokarinsu wajen ganin an sake su nan take.

Shugaban ya kuma umarci hukumomin gwamnati da abin ya shafa su bayar da goyon baya ga iyalan yaran da aka sace.

Sama da dalibai 200 ne ‘yan bindiga suka sace a Tegina, karamar hukumar Rafi a ranar Lahadi.

Makarantar Islamiyya tana da bangarori uku da suka haɗa da Nursery, firamare, da ƙaramar makarantar sakandare.

Gwamnatin Niger Ta Dauki Mataki

A halin yanzu, Gwamnatin Jihar Neja ta ba da tabbacin cewa suna daukar matakan tabbatar da sakin yaran makarantar.

Mataimakin gwamnan jihar, Ahmed Ketso yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati ya ce ana kokarin gano bakin zaren.

Ketso ya ce duk da cewa ba a tabbatar da yawan yaran makarantar da aka sace ba, amma kokarin da jami’an tsaro ke yi don ganin an sake su ya tsananta.

Ya ce akwai makarantun gwamnati da yawa a Tegina amma gwamnati ta himmatu wajen cire makarantun kwana kuma ta tabbatar kowace makarantar Firamare da Sakandare tana da jami’an tsaro.

Ya ba da tabbacin cewa dabarun suna kan yadda za a saki wadanda aka sace kamar yadda aka saki na yaran Kagara inda aka yanke hukuncin biyan kudin fansa.

“Bama biyan kudin fansa ga masu satar mutane. Muna kokarin tattaunawa domin ganin yadda za mu dawo da su lafiya, ”inji shi.

Ya ce gwamnati ta tuntubi wasu iyayen da aka gano na yaran da aka sace, inda ta ba su tabbacin dawowar su lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *