Da dumi dumi: Daga ƙarshe bayan kai ruwa rana, an ceto masu sallar Tahajjud guda 30 da ƴan bindiga suka sace.

Tun da fari dai, wata haɗakar rundunar sojoji, ƴan sanda, da sauran jami’an tsaron sakai ne suka haɗa gwuiwa domin gudanar da ɗan ƙwarya ƙwaryan aiki tare.

Inda Allah cikin ikon sa, sai gashi sun samu nasarar ceton mutanen guda 30 cif-cif.

Idan za’a iya tunawa tun da fari, ƴan bindiga sun dirar wa masallata ne guda 30 , yayin da suke faman zabga ibada salon Tahajjud a talatainin daren watan Ramadan mai albarka.

Lamarin ya faru ne a Zurumin Zamfara, garin da yake iyaka da boda wato wajen garin dajin jibiya.

Mai magana da yawun hukumar ƴan sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isah, ya tabbatar da kamawa gamida sakin mutanen.

A cewar SP Gambo, yan bindigar suna da yawan gaske, kuma sunyi ƙoƙarin kewaye masallacin ne , wanda sukayi nasarar yin hakan.

Sai kuma, suka umarci kowa da ya bada haɗin kai, wanda daga ƙarshe suka tasa ƙeyar su, da sunan sun sace su.

To amma Allah cikin ikon sa, an samu nasarar amso su.

Duk da cewa babu wani bayani, dangane da ko an biya kuɗin fansa ko bata kashi akayi.To Allah ya kyau ta!

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *