Da Dumi Dumi: Yanzu haka, Boko Haram sun mamaye sansanin sojoji a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno.

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da safiyar Lahadi sun mamaye kauyen Ajiri na karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno, inda suka samu damar shiga sansanin sojoji tare da fatattakar sojoji.

Wannan harin na zuwa ne kimanin awanni 12 lokacin da wasu gungun mahara suka kai hari a ranar Asabar a Rann, Hedikwatar karamar hukumar Kala Balge da kauyen Limankara na karamar hukumar Gwoza da ke jihar.

Garin Ajiri mai kimanin kilomita 50 daga tsakiyar Borno, yana kan hanyar Maiduguri zuwa Mafa-Dikwa tare da dubban mutanensa, galibi ‘Yan Gudun Hijira (IDPs) da aka sake komawa kwanan nan zuwa cikin garin don karbar yankansu.

Wata babbar majiyar tsaro ta tabbatar da shigowar maharan zuwa sansanin sojan Ajiri, Rann da al’ummomin Limankara, duk da cewa ya ce, har yanzu bayanai kan hare-haren ba su da kyau a lokacin da ake hada su.

Cikakkun bayanai zasu zo Nan gaba….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *