Da Dumi dumi: Yanzu haka ‘yan Boko Haram sun kutsa cikin karamar hukumar Gubio ta jihar Borno suna harbe-harbe.

Yanzu Haka Kowa ya tsere gida a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno sakamakon karar harbe-harbe da ake ji wanda ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka shiga Garin.

Wani mazaunin karamar hukumar ta Gubio wanda muka sakaya sunansa ya shaidawa Jaridar Mikiya cewa sun yi sallar azahar kenan suna cikin yin Addu’a sai suka fara jin karar harbe-harbe, wanda hakan ya tilasta musu gudu zuwa gidajensu.

Yanzu haka dai kowa yana gida yana fargaba, yayin da ake ta jin karar harbe-harbe babu kakkautawa.

Muna tafe da karin bayani…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *