Dabarar mu ita ce, munso ace an ɗan rasa ɗalibai kaɗan, ta hakan mu kuma sai mu cillawa masu garkuwa da mutanen boma bomai a maɓoyar su — El-rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai yace dabarar ceto ɗalibai 29 na Afaka itace, a cillawa masu garkuwa da mutanen boma bomai a maɓoyar su, a ceto wasu daga cikin su sannan a saki wasu daga cikin ɗaliban, su kuma masu garkuwa da mutanen a tashe su aiki baki ɗaya.


Jaridar The Punch ta rawaito cewar, El-rufai yayi wannan batu ne a 6 ga watan Mayu, a wani salon yanar gizo-gizo da “African Leadership Group” suka shirya. Ya bayyana haka ne da aka tambaye shi, ko me yasa yaƙi yarda da ya tattauna da masu garkuwa da mutane.


Yayin amsa tambayar, El-rufai sai ya zayyano dabarar da cewa, bata samu nasara ba sakamakon masu garkuwa da mutanen sun kubucewa narkon wutar zaratan Sojojin Najeriya

Ga kalaman El-rufai:

“Kwana biyu da sace ɗaliban Afaka, sojojin sama sun tabbatar min da cewa sun san maɓoyar masu garkuwa da mutanen, wato gurin da ake riƙe da ɗaliban, kuma sojoji sun riga da sun ɗana tarko”.

“Muna da niyyar kai musu farmaki. amma munsan cewa, zamu rasa ɗalibai kaɗan, ta hakan mu kuma sai mu cillawa masu garkuwa da mutanen boma bomai a maɓoyar su mu kashe su duka, sannan wani yanki na ɗaliban tabbas zasu dawo. Itace dabarar da sojojin sama dana ƙasa suka yanke…


Amma ina, hakan bai yiwu ba, domin sun kuɓuta da narkon wutar sojojin mu. Wannan shi yasa bamu kai musu farmaki ba.


“Mun san cewa abune mai hatsarin gaske, amma kuma a ƙoƙarin yin, zamu iya rasa waɗanda aka sace ake garkuwa dasu ɗin, amma shine farashin aikin da zamu iya biya. Yaƙi ne wannan, kuma a yaƙi kowa yana cutuwa ne, kuma bazamu taɓa biyan kuɗi a yaƙi ba, biyan kuɗin bazai taɓa warware mana matsalar ba, kuma haka abin yake a ko ina cikin duniya”.

To sai dai Gwamnan yace, “Ya rasa ƙiba”saboda rashin tsaron dake addabar mutanen jihar Kaduna, domin ko barci baya iya yi da daddare. Bugu da ƙari, yace rashin tsaro a Kaduna, wasan yara ne idan aka haɗa da rashin tsaron dake addabar mutanen jihar Katsina, Niger da kuma jihar Zamfara.


Sai dai ya zargi kafafen watsa labarai da cewar, sunfi maida hankali ne ga jihar sa, saboda a cewar sa, yafi daidaita da yanayin abinda suke bada labari akai na rigimar ƙabilu ƙabilu.

El-rufai ya nanata cewa, akwai sanda ƙauye guda aka tarwatsa a jihohin Naija da Katsina sakamakon aikin masu garkuwa da mutane da ɓarayin daji amma hakan ai bai taɓa faruwa ba a Kaduna.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *