Dole sai kun tashi tsaye sannan za a shawo kan matsalar tsaron Najeriya – Sabon Hafsan Sojin Najeriya ya gadawa kwamandojin Soji.

Sabon hafsan sojin kasa ya ce sai sojoji sun tashi tsaye za a shawo kan matsalar tsaro a Najeriya
Janar Farouk.

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya, ya ce ya ɗaura ɗamarar ƙara gina rundunar sojin ƙasar, bisa turbar iya aiki, da shirya cim ma duk wani buri na kare Najeriya da martabarta, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Amma ya ce hakan ba zai samu ba, sai sojojin Najeriyar sun ƙara tashi tsaye, tare da bunƙasa shirye-shirye da dabaru, waɗanda za su dace da irin sauyin da ake samu a fagen daga.

Manjo Janar Yahaya ya bayyana hakan ne a yayin taron farko na yini guda da kwamadojin rundunoni da kwamandojin fagagen daga, da dai sauran manyan jami’an rundunarsa, a hedikwatar sojan Najeriya da ke Abuja a yau Litinin.

A wajen taron, shugaban sojin ya bayyana aniyar ƙara kyautata ayyukan rundunar, da kuma bin hanyoyin duk da suka dace, don tunkarar matsalar tsaro da ke addabbar sassan kasar.

Sannan ya ce wajibi ne rundunar sojan kasar ta ci gaba da tsare tsattsaurar ɗabi’a da ƙa’ida irin ta aikin soja, don cim ma nasara.

Manjo Janar Farouk Yahaya, ya kuma yi nuni cewa, ‘Hannu daya ba ya daukar jinka’.

“Abin da ke tafe da ni yanzu shi ne na haɗa ƙarfi da ƙarfe na yi aiki tare da sauran ƴan uwa da jama’a daga dukkan fannoni kamar ɓangaren koyarwa da na atisaye da na na sojin sama da na ruwa ƴan sanda da sauran masu ruwa da tsaki.

“Idan aka samu kyakkaywar niyya da ƙudurin yin aiki in Allah Ya yarda za mu yi nasara,” a cewarsa.

Wani muhimmin abu da sabon hafsan mayaƙan ƙasa na Najeriyar yake ganin zai taimaka wajen yaƙi da masu aikata miyagun laifuka a ƙasar, shi ne irin ingantacciyar gudunmawar da jama’ar garuruwa za su bayar.

“Mutanen nan yanwancinsu a cikinmu suke, don haka sai an samu zarata da za su iya bayar da rahoto kuma a lokacin da zai yi amfani.”

Sabon hafsan mayakan kasan na Najeriyar dai ya hau kujerar wannan muƙami ne, yayin da kasar ke fuskantar ɗumbin kalubalen tsaro, da ya haɗa da rikicin Boko Haram, da masu tayar da ƙayar baya, da ‘yan bindiga, da masu sace mutane don neman kuɗin fansa da dai sauransu.

Jama’a kuma na nan cike da kyakkyawan fatan, ganin rundunar tasa ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, wajen tunkarar wannan ƙalubale da murƙushe matsalar.

BBC HAUSA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *