Duk da cewa ta hana yin tashe, hukumar ƴan sanda a jihar Kano ta kama masu yin tashe suna yin kuma ƙwacen waya.

Idan za’a iya tunawa kakakin hukumar ƴan sanda a ƴan kwanakin baya ta bakin , DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta sanar da hana tashe a kafatanin jihar Kano.

Kamar kuwa sun san za’a aikata hakan, domin a yau ma kakakin hukumar ya sanar da cafke wasu matasa da suka fake da guzuma suna harɓin karsana.

Mai magana da yawun hukumar, yace matasan sun fito ne ɗauke da muggan makamai, kuma daga sassa daban-daban na jihar Kano.
Matasan ɗauke da makamai suna tashe ne, inda daga bisani suka sauya akalarsu zuwa ƙwacen wayoyin waya da karfin tsiya da tsiyaryaki.
DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ƙara da cewa, da zarar sun ƙwaci wayar, matasan na bin mutane da sare-sare ta hanyar amfani da adduna da kuma wuƙaƙe.
Haka zalika, hukumar ta sanar da nasarar masu faɗan daba, da kuma masu satar wayoyin hannu a cikin baburan adaidaita sahu waɗanda aka fi sani da Keke Napep.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *