Gwamnatin Legas Ta Sassauta Dokar Hana Fita….

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanyo-Olu, ne ya Sanar da hakan a Lokacin da yake Rangadin ganin Irin Ta’asar da Masu zanga zangar sukayi a Jihar.

Sanyo-Olu, yace Daga gobe Asabar ne dokar Zata fara aiki, kowa ya Fita daga Karfe 8 na Safe, zuwa 6 na Yamma, Har zuwa Ranar Litinin kafin a duba Yiwuwar kara Sassauta Dokar.

Gwamnan yace Ba’a taba yiwa Jihar Barna da Hasara Kwatankwacin wannan ba tun kafuwar Jihar.

Da farko dai Zanga zangar ta Lumana ce Amma Daga bisani ta Rikide ta koma Ta’addanci, bayan Masu zanga zangar sun zargi cewa Jami’an Tsaro sun Afkamusu a Ranar Talata da ta gabata a Dai dai Lekki Toll Gate, abin da Ya Sanya zanga zangar ta Chanza zuwa Ta’addanci kenan.

Ahmed T. Adam bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.