Gwamnonin Najeriya musamman na Arewa sune matsalar tsaron kasarnan__Janar Ibrahim Badamasi Babangida yakara nanawata.

Biyo bayan kone gidaje sama da 70 da kuma kwashe mutane sama da 60 da ‘yan Bindiga suka kumayi a jihar Zamfara, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kara nanata maganarsa.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kara tabbatar wa da shugaba Buhari cewa matsalar rashin tsaron kasar nan da aketa fama da ita gwamnonin kasar nan ne fa.

Babangida ya kara da cewa matukar shugaba Buhari bai bullowa gwamnonin kasar nan ta bayan Gida ba to tabbas za su jefa kasar nan cikin halin da shi kansa bai taba tsammani ba a karkashin mulkinsa.

Babangida ya ce dole sai shugaba Buhari ya tilastawa gwamnonin kasar nan musamman na Arewa cire siyasa a lamarin tsaron kasar nan in ba haka ba kuma za ai ta yin tufka da warwara ne kawai.

Babangida ya ce duk wani mataki da gwamnatin Tarayya za ta dauka akan lamarin tsaron kasar in dai ba a tura kaso 70 daga cikin 100 na matakin da za a dauka akan gwamnonin kasar nan musamman na Arewa ba, to ci gaban mai hakan’ rijiya za ai ta yi kawai.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *