Hare-hare: Duk ‘Yan Bindiga Da Aka Kame A Anambra ‘Yan Kabilar Ibo Ne – Gwamna Soludo

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana sunayen ‘yan bindigar da ke ta’addanci a sassan jihar, inda ya ce duk wadanda aka kama ‘yan kabilar Igbo ne.

A baya-bayan nan ne ‘yan bindiga suka kaddamar da ta’addanci a yankin Kudu-maso-Gabas inda suke auna mazauna, jami’an tsaro, da kayayyakin more rayuwa.

Yawancin hare-haren dai ana alakanta su da ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da kuma reshenta na ‘yan ta’adda, wato Eastern Security Network (ESN).

Da yake mayar da martani kan hare-haren a yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Soludo ya ce gwamnati mai ci a Anambra ta samu nasarar kawo matsalar tsaro a jihar zuwa mataki mafi karanci.

“Bari na fito fili a kansa; 100% na mutanen da muka kama ’yan kabilar Igbo ne. Ba wai wasu mutane ne suke kutsawa daga wani wuri ba; 100% ’yan kabilar Igbo ne kan ’yan kabilar Igbo, wannan shi ne gaskiya,” inji gwamnan.

“Kashi 100 na mutanen da muka kama su ‘yan kabilar Igbo ne daga sauran jihohin kudu maso gabas kuma ba kowa daga Anambra ba.

“Amma yayin da muka ci gaba, sai muka gano cewa yawancin matasan da aka kai su wadannan ciyayi da aka cusa aka kuma fara shiga cikin irin wadannan abubuwa su ma ‘yan asalin jihar Anambra ne.”

Kafin Farfesa Soludo ya karbi ragamar shugabancin jihar, mazauna Anambra sun kasance cikin fargaba saboda da kyar mako guda ya wuce ba tare da an samu rahoton harin ba.

Ya shaida wa gidan talabijin na Channels a ranar Lahadin da ta gabata cewa lamarin tsaro ya samu sauki sosai, kuma ya danganta hakan da kokarin jami’an tsaro.

“Bayan inda abubuwa suka kasance lokacin da muka zo, ba muna cewa Anambra tana da 100%…

“An lalata sansanoni goma sha biyar (wanda ‘yan bindiga ke gudanarwa) a nan (an lalata su). Ko a jiya (Asabar) wasu wuraren (inda) suke taruwa sun lalace; mun lalata kayan aikinsu kuma ba na tsammanin suna da karfin sake zuwa da irin ta’asar da suka yi a baya,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *