Idan Gwamnatin Tarayya da gaske take, za mu iya kawar da tayar da kayar baya cikin watanni shida, inji Sanata Ndume.

Majalisar dattijai a ranar Talata ta yi Allah wadai da Shugaba Muhammadu Buhari kan matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a fadin kasar, musamman a arewa maso gabas.

Zaman ya kasance ne gaba daya game da kisan gillar da aka yi wa manoma a ranar Asabar a garin Zabarmari da ke cikin Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno da ’yan Boko Haram suka yi.

Ba sanatoci kaɗan ne suka keɓe kalamai masu zafi ga Buhari ba, ciki har da Ahmed Baba Kaita mai wakiltar Katsina ta Arewa, yankin shugaban kasa.

A nasa gudummawar, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Ali Ndume, wanda ya fito daga jihar Borno da ke fama da rikici ya zana halin da sojoji ke ciki a fagen daga har ta kai ga ana zargin ba su da wasu kayan aiki.

“Sojoji a na gaba wajen gudanar da ayyukan suna raba alburusai. Ba su da kyan aiki. Wasu daga cikinsu ba su da hular kwano ko rigar sulke.

“Ba su da sabbin bindigogi AK-47 a fagen daga. Masu tayar da kayar baya sun fara neman haraji don bai wa manoma damar shiga gonaki.

“Boko Haram sun fara sanya shingaye a hanya. Idan Gwamnatin Tarayya da gaske take, za mu iya kawar da tayar da kayar baya cikin watanni shida, ”inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.