Ina da yaƙinin Nigeria zata shawo kan matsalar tsaro nan bada jimawa ba ~Obasanja

Tsohon Shugaban ƙasar ta Nigeria, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana da yaƙinin za’a shawo kan matsalar tsaro a Nigeria.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani taro na musamman da aka saba shiryawa karo 108 domin karrama shi tare da Shugaban ƙungiyar kiristoci ta ƙasa (CAN) mai suna Dr Samson Ayokunle; wanda ya gudana yau Laraba a garin Oshogbo ta Jihar Ogun.

Cikin ɗan taƙaitaccen jawabin da ya furta yayin taron; Obasanjo ya bayyana cewa nan bada daɗewa ba Nigeria zata kawo ƙarshen matsalar tsaron data addabi al’umma, “kamar yadda jaridar Punch ta bayyana”.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *